Daliban jami’ar jihar Kaduna KASU sun gudanar da zanga-zanga jiya a kofar shiga makarantar domin nuna rashin jin dadinsu kan yadda hukumar makarantar take nuna halin ko-in-kula wajen samar wa daliban tsaro yadda ya kamata a makarantar.
Daliban sun koma da yadda ‘yan daba suka addabesu a makarantar kuma babu wani himma daga hukumar jami’ar na ganin ta samar wa daliban tsaro.
Wani dalibi cikin masu zanga-zangar da baya so a fadi sunansa ya ce ” Abin ya fara fin karfin mu yanzu. Kusan kullum sai an shiga anyi mana sa ta wasun mu ma kwace a keyi mana kuma babu wani abinda hukumar makaranta take yi akai.”
Daliban sun dauki tsawon awoyi uku suna zanga-zangar da ya jawo kusan rufe titin Tafawa Balewa da ke cikin Kaduna.