Mataimakin shugaban kungiyar likitoci reshen birin tarayya Abuja Wisdom Ihejieto ya sanar da cewa adadin yawan mutanen da suke dauke da cutar dake lahanta hantar mutum wato Hepatitis a kasa Najeriya ya kai miliyan 20.
Ya fadi hakan ne yayin da yak e zantawa da shugaban kamfanin dillancin labarai Bayo Onanuga ranar Talata a Abuja.
Ihejieto ya ce akan kamu da cutar Hepatitis ne idan wata kwayar cuta ta harbi hantar mutum.
Ya ce sun gano yawan adadin mutanen da ke dauke da cutar ne bayan binciken da suka gudanar daga takardun asibitocin gwamnati da kuma wadanda suke zaman kansu a fadin kasa Najeriya.
Ihejieto ya ce cutar ta na yawan kama ma’aikatan asibiti saboda mafi yawan kayan aikinsu masu kaifi ne sannan kuma saduwa da juna a tsakaninsu ya kan yi yawa.
Ihejieto ya ce ana kama cutar ne ta hanyar jima’I, amfani da kayan wanda ke dauke da cutar kamar chokali, kofi, reza ta yankan kumba, sumbatar wanda ke dauke da cutar, tari da shakar iskar juna.
Ihejieto y ace saboda hakan ne suka niki gari ta musamman domin samun goyan bayan shugaban gidan jaridar wajen wayar da kan mutane akan cutar da kuma yadda za a iya gujewa kamuwa da cutar.
Tony Philips ya ce cutar Hepatitis ya fi cutar Kanjamau lahani sannan yayi kira ga masu fada aji da su zo a hada hannu gaba daya domin kawo karshen wannan cuta ta Hepatitis.
Daga karshe kungiyar ta amince da ta ware ranar 27 gawatan Mayu domin taron wayar da kan mutane akan cutar Hepatitis.