Fadar shugaban kasa ta yi tir da yadda tsohon gwamnan jihar Kaduna Dangiwa Umar yake caccakar ayyukan gwamnati musamman akan yaki da cin hanci da rashawa da takeyi a kasa Najeriya.
Kakakin shugaban Kasa Mal. Garba Shehu ne ya sanar da hakan a martini da ya maida wa tsohon gwamnan.
Dangiwa Umar ya ce “ Dakatar da sakataren gwamnatin tarayya da shugaban kasa yayi abu ne mai kyau kuma ya cancanci a yabo.
Ya zargi shugaban kasa da nuna kiyayyarsa karara akan Sambo Dasuki saboda wai ba inuwarsu daya ba kuma don yayi aiki da shugaban kasa dan kabilar Ijaw.
Garba Shehu yace irin wadannan maganganu da irin su Dangiwa Umar sukeyi ba zai sa gwamnati ta karkata akalarta ba akan abin da ta sa a gaba.
“ Da yawa daga cikin manyan kasar nan basu jin dadin yadda wannan gwamnati ta ke gudanar da ayyukanta. Duk a takure suke saboda ba yadda suka saba bane abubuwa ke faruwa a kasa yanzu.
“ Duk da adawar da ake yi wa gwamnati a kafafen yada labarai, har yanzu irin wadannan mutane basu kawo wani hujja ko da guda daya ne da yake nuna cewa Buhari na yin zabe a yakin sa na cin hanci da rashawa ba.
“ Buhari bai taba kokarin nuna son kai ba ko kuma ya ce wannan dan mowa ne waccan dan bowa ne a wannan tafiya da akeyi yi.