Kakakin rundunar sojin Najeriya Janar Sani Usman ya ce babban hafsan sojin Najeriya Janar Tukur Buratai ya na jinjina wa dakarun sojin Najeriya da suke filin daga a sansanoni dabam dabam dake jihar Barno.
A sakon da Buratai ya aikawa sojojin, ya ce kasa Najeriya ba za ta taba mantawa da sadarkar da rayukan da dakarun su keyi wa kasa Najeriya ba musamman wajen fafatawa da Boko Haram.
Janar Sani ya fadi hakanne a wata sako ta musamman daga babban hafsan sojin, janar Buratai wanda ya saka wa hannu.
Buratai ya fadi hakan ne a ziyarar da ya kai wa wasu dakarun sojin Najeriya da ke garuruwan Pulka da Gwoza, jihar Barno.
“Kasa Najeriya na bugun kirji da ku kuma ina so kusa ni cewa tarihi ba zai taba mantawa da irin sai da rayukanku da kukayi wa kasar ba.’’
“Za kuma mu ci gaba da samar muku da duk ababen da kuke bukata domin ganin cewa an kawo karshen Boko Haram da kuma samun damar komawa da ‘mazauna sansanonin ‘yan gudun hijira da ke fadin jihar garuruwan sun a asali.”
Daga karshe ya shawarci dakarun sojin da su daure damtse domin ganin sun kamo duka shugabannin kungiyar Boko Haram.