Shugaban Kasa muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyar sa ga Iyalan marigayi Alh. Ahmadu Chanchangi da kuma ga gwamnati da mutanen jihar Taraba da na Kaduna in da ya zauna tsawon rayuwarsa.
Buhari ya jinjina wa marigayi Ahmadu chanchangi akan irin ayyukan da yayi na taimaka wa jama’a musamman talakawa.
Yace za’a dade ana juyayin rashin marigayin.
Ya roki Allah da yaji kan sa ya kuma sa Aljannan ta zamo makomarsa.