Buhari da jam’iyyar APC sun yi watsi damu, ‘yan Jihar Taraba – Inji Aisha Alhassan

0

Ministan harkokin mata Aisha Alhassan ta ce Buhari da jam’iyyar APC sun yi watsi da mutanen jihar Taraba kwata-kwata tun bayan zabe.

Minista Aisha tace bayan ita da aka nada Minista, da kuma wani da ka bashi mukamin jakada babu wani kujera da aka ba wani dan jam’iyyar daga jihar Taraba.

“ Da ace jam’iyyar APC ce ke mulkin jihar Taraba da ni kai na bana Abuja.

“ Ya’yan jam’iyyar a jihar sun koka da yadda ake nuna halin ko in kula da al’amuran su a jihar wanda hakan ne yasa mu ka zo nan domin mu fada wa jam’iyyar damuwar mu.

Babu wata jam’iyyar adawa da tayi abin da mukayi tun 1999. Amma bayan ofishoshi biyu da na ambata an ba mu babu wata kujera da aka nada dan jam’iyyar daga Taraba. Hatta ayyukan gwamnatin tarayya da a keyi a jihar ba’a neman shawaran mu a kai.

Share.

game da Author