Boko Haram sun kai wa sojin Najeriya harin bazata

0

Sama da ‘yan Boko Haram 200 ne suka far ma wata bataliyan sojojin Najeriya a bazata in da suka kashe sojoji 8 sannan suka raunata wadansu 11.

Kamar yadda muka jiyo daga majiyar mu Boko Haram din sun yi wa bataliyan sojin shigar ba za ta ne .

Sojin Najeriya sun yi arangama da Boko Haram din a batakashin da ya dauki kusan awa daya ana gwabzawa.

Da wuta tayi wuta dai Boko Haram sun koma da baya inda wasunsu suka gudu da raunuka a jikinsu. Sun tafi da makamai da yawa na sojojin Najeriya.

A bayanan da muka samu kuma ya nuna cewa Sojojin Najeriya sun Kashe ‘yan Boko Haram a artabun da akayi.

Da muka ne mi sani ta bakin kakakin rundunar sojin Najeriya Birgediya Janar Sani Usman, duk wayoyinsa ba a amsa suba sannan wasikun da muka tura masa shima ba’a a aiko da amsoshinsu ba sai dai wani jami’ain soji ya sanar damu cewa Janar Lucky Irabor yana cikin wata mitin ne a lokacin da muka kira lambar sa.

Share.

game da Author