Gwamnatin Birtaniya ta ce za ta bayyana sunayen ‘yan Nijeriya wadanda suka mallaki manyan kadarori a Ingila.
Hakan ya fito ne daga bakin Babban Sakataren Kwamitin Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Dakile Cin Hanci, Bolaji Owosanoye.
Birtaniya tace zata fadi hakanne cikin shekara mai zuwa.
Babban Sakataren dai ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na NAN cewa, an yi nisa wajen cim ma wannan yarjejeniya a tsakanin kasashen biyu.
Owosanoye ya kara da cewa wannan mataki da kasashen biyu suka dauka, wani yinkuri ne wajen kara himmar hana cin hanci da rashawa a kasar nan.
“Ko shakka babu cewa manyan baragurbi da gurbatattun ;yan Nijeriya sun kassara al’ummar kasar nan, sun talauta jama’a ta hanyar wawure dukiya, wanda y ace hakan kuwa tilas sai an tashi tsaye an hana aikata wannan laifi.”
“Mu na so mu tabbatar da cewa babu wata kasa ko wani wuri da duk wanda ya wawuri dukiyar al’umma zai gudu ya tsira, ko zai gudu ya boye dukiyar da ya sace.”
“Gwamnatin Birtaniya dai ta tabbatar mana da cewa cikin 2018 za ta bayyana sunayen duk wani dan Nijeriya da yake da wata kadara da kuma inda kadarar ta ke a cikin kasar ta. Wadannan kuwa sun hada har da gidaje da lambobin asusun ajiyar bankunan su, musamman saboda sun guje wa biyan haraji, kuma sun kasa bayyana wata gamsashshiyar hanyar da suka samu kudaden.”