Jaruma ‘yar wasan fina-finan Hausa, Nafeesat Abdullahi ta ce bata aske gashin ta ba kamar yadda ake ta yada wa a gari.
Nafeesat ta saka wata hoton ta ba gashi a kanta a shafin ta na Instagram inda ta yi ma hoton suna ‘ Na Dawo’.
Ganin yadda hoton ta ke ta yawo a shafunan mutane a yanar gizo da irin nuna rashin jin dadin haka da ga wasu masoyan jarumar, Nafeesat ta sanar cewa bata fa aske gashin ta.
Ta fadi hakan ne a shafin ta na Facebook in da ta ce wannan hoto na wani sabon shirin ta ne.
“Ban Aske Gashi Na Ba, Gashi Na Yana Nan Daram, Ga Masu Yada Jita Jita Wai Na Aske Gashi Na Saboda Film.”