Gwamnan jihar Kaduna Mal. Nasir El-Rufai yace ba’a taba hana shi shiga fadar shugaban kasa, Aso Rock ba.
El-Rufai ya fadi da hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai bayan tasowa daga sallar Juma’a dayayi tare da shugaban kasa a Aso Rock.
Anyi ta yada rade-radi cewa an hana El-Rufai shiga fadar shugaban kasa tun bayan wasikar da ya rubuta wa shugaba Buhari.
El-Rufai yace babu wanda ya isa ya hana shi shiga fadar shugaban kasa.
Gwamnan yace ya rage zuwa fadar shugaban kasa ne saboda Buhari na bukatan hutu dalilin da yasa kenan ya ke dan daukar lokaci kafin ya zo Aso Rock din.
“ Babu wanda ya ta ba hani shiga fadar shugaban kasa kuma babu wanda ya isa ya hani zuwa ko shiga.
“ A matsayina na gwamna bani da shamaki da fadar shugaban kasa, babu wanda zai bincike ni, kawai na ga ya kamata ne in dan daga kafa domin ya samu hutun da yake bukata.
“Shugaban kasa yana bukatan lokaci sosai domin samun hutu saboda ganawa da mutane ya na daga cikin abubuwan dake gajiyar da shugaba.
“ Ni gwamna ne kuma a duk lokacin da na gana da mutane a kalla 10 a rana na kan gaji. Ba yawan takardun da zaka sa ma hannu bane ke gajiyar da shugaba, mutanen da ke shiga da fita su ne ke gajiyar da kai.
“ Bana so in takura ma shugaban kasa wajen zuwa kullum amma muna ganawa da shi.
Daga karshe El-Rufai ya roki ‘yan Najeriya da su daga ma shugaban kasa kafa ko ya dan dinga samun hutu mai makon ayi ta bibiyar sa har ofis.
“ Bamu taba samun matsala ba da shugaban kasa domin ko jiya mun hadu. Tsakanina da shugaban kasa kamar da ne da uban sa ku hakan wani abin alfahari ne ga reni.
Discussion about this post