Tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu da dan takaran gwamnan jihar Neja a jam’iyyar PDP a zaben 2015, Umar Gado Nasko za su ci gaba da zama tsare a hukumar EFCC kamar yadda Alkali Mohammed Mayaki na babban Kotun Shari’a dake jihar ya yanke.
Hukumar EFCC na tuhumar Babangida Aliyu ne da laifin yin babakere da kudadaen jihar a lokacin da yake gwamnan jihar.
Za’a ci gaba da sauraron shari’ar ranar 4 ga watan Mayu.