Shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki yace bashi da ikon janye dakatarwar da majlisa tayi ma sanata Ali Ndume ba.
Saraki ya fadi hakanne da yake amsa tambayoyi daga manema labarai bayan ganawa da yayi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadar gwamnati
Tun bayan dakatar da Ndume, manyan masu fada a ji, ciki har da gwamnan Jihar Barno Kashim Shettima sun a ta rokon Saraki da ya janye wannan dakatarwa da aka yi wa Sanata Ndume.
Sai dai kuma bayan kammala taron sirri da Saraki ya yi da Shugaba Buhari, ya bayyana wa manema labarai a fadar gwamnati cewa, ‘’ina ma a ce ina da ikon janyewa din.’’
Ya ce shi da kakakin majalisar wakilai ba su da ikon yin wani abu na kan su, sai abin da majalisa ta amince da shi.
Majalisar dattijai ta dakatar da sanata Ndume ne saboda shine ya nemi majalisar da ta binciki badakalar siyan motar da ake zargin shugaban majalisar Bukola Saraki da siya ba tare da takardu na ainihi ba da kuma zargin cewa wai sanata Dino Melaye bai gama karatun jami’a ba.
Kwamitin da ta binciki wannan korafi sannan ta mika sakamakon bincikenta a zauren majalisar ta kuma sanar wa majalisa cewa sanata Ndume ya yiwa majalisar karya.
Kwamitin ta ba da shawarar a dakatar da Ali Ndume na shekara daya, in da bayan haka majalisar ta amince da dakatar dashi na wata shida.