Ba mu da Asusun Tsaro a jihar Kaduna – Inji El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna Mal. Nasir El-Rufai yace jihar Kaduna bata da wata asusu ta musamman da yake ajiye wai na tsaro.

Gwamnan ya fadi hakanne a wata mai da martini da yayi wa Kakakin majalisar wakilai Yakubu Dogara da ya nemi ya sanar wa duniya kudaden da yake samu na tsaro da na kananan hukumomi da yadda yake kashe su.

El-Rufai ya ce ya san hakan zai ba mutane mamaki cewa da yayi wai jihar bata da wata asusu na tsao amma kuma hakanne.

“ Kasafin kuden jihar mu yaba da bayanai akan kudaden da muke samu da kuma irin wadanda ke tafiya harkar tsaro kuma wadannan kudi ba kudade bane da gwamna ke kashe wa.

“ Yadda muke kashe kudin mu ba yadda Majalisar Kasa bane suke kashe nasu. Domin su suna kashe kudadensu ne ta yadda babu wanda ya san gaban su ko bayan su. Komai a boye su ke yi ta inda hatta ‘yan majalisar ma basu san menene ake samu ba ballantana su san yadda ake kashe su.

El-Rufai ya yi kira ga majalisar da ta bude kasafinta kowa ya san yadda take kasafta shi da kashe su.

Kakakin gwamnan jihar Kaduna ne ya Samuel Aruwan sanya ma wannan takarda hannu a madadin gwamnan jihar.

Share.

game da Author