Ba da yawu na bane Jimeta ya yi magana, ni ina tare da APC dari bisa dari – Inji Bindow

0

Gwamnan jihar Adamawa, Jibirilla Bindow ya ce ba da yawun sa bane shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar AbdulRahman Jimeta yayi magana a taron jam’iyyar APC na shiyar Arewa Maso Gabas.

Shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Abdulrahman Jimeta ya ce reshen jam’iyyar a Adamawa na fushi da uwar jam’iyyar ta kasa musamman akan yadda tayi watsi da mutanen jihar Adamawa da nuna musu wariya da mulkin Buhari ta ke yi wajen nade-naden ofisoshin gwamnati a Abuja.

Ya ce idan har ba’a gyara ba za su iya ficewa daga jam’iyyar APC.

AbdulRahman ya fadi hakan a gaban gwamna Bindow kuma bai hana shi ba a wajen taron jam’iyyar na shiyar Arewa Maso Gabas a Yola.

Jimeta ya ba tawagar sako zuwa ga uwar jam’iyyar ta kasa cewa “ Muna nan muna yi mata biyayya amma fa ta sani cewa ko addine ne mutum ya gaji dashi yakan iya canza shi.

“ Ku gaya musu cewa bukitin mu ya fara cika, musamman ganin cewa basu damu da halin da muke ciki ba, mu ne sojojin jam’iyyar kuma mune ya kamata mu amfana da jam’iyyar amma idan har suka ki yin komai a kai za mu canza sheka zuwa jam’iyyar adawa.

“Gwamnatin tarayya ba ta ne man shawaran mu anan idan za tayi nade-naden ta musamman wanda ya shafi jihar Adamawa.”

Gwamnan jihar Jibirilla Bindow ya yabi shugaban Jam’iyyar ta su na kasa John Oyegun sannan yace za su ci gaba da yi wa jam’iyyar biyayya.

Domin Kara jaddada hakan gwamnan ta bakin Kwamishinan yada labaran jihar Ahmad Sajoh ya ce maganar da Jimeta yayi da bam na sa da bam.

Ya ce gwamna Bindow bai ce zai fice da ga jam’iyyar APC ba kuma baya tare da Jimeta akan hakan.

Ya ce da gwamnan da gwamnatin jihar na goyon bayan ayyukan da uwar jam’iyyar ta kasa ta keyi da mulkin shugaban Muhammadu Buhari.

Share.

game da Author