‘Yan Najeriya sun nuna jin dadin su akan karramawar da gidan jaridar PREMIUM TIMES ta samu na zama daya daga cikin gidajen jaridun da suka fallasa badakalar ‘Panama Papers’ wanda hadin guiwa ne na gidajen jaridu 100 a kasashen duniya.
A wata sako ta musamman da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai yayi wa gidan jaridar yace wannan karramawa abu ne wanda ya kamata a jinjina ma gidan jaridar Premium Times.
“ Wannan karramawa ya nuna irin kokari da wannan gidan jarida take yi wajen koyar da matasa aikin jarida da ya jibanci kawo labarai da zai taimaka wajen samarda hanyoyin da zai kawo karshen matsalolin da mutane ke fama dasu.
“ Ina taya ku murna da fatan zaku ci gaba da samar da labarai da da zai samar da ci gaba a kasa Najeriya.
Tsohon Mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar shima ya aika wa kamfanin sakon taya murna akan wannan karramawa da ta samu.
Sauran wadanda suka aiko da irin wannan sako sun hada da: Dele Olojede, Phillip van Niekerk, Innocent Chukwuma, Kole Shettima, Joseph Amenaghawon, Dayo Aiyetanda Ms. Motunrayo Alaka
Gidan Jaridar PREMIUM TIMES ta samu karramawa ta ‘Pulitzer Prizes’ na kasar Amurka saboda bincike da wallafa bayanai akan wasu jiga-jigan ‘yan Najeriya da na kasashen duniya da suke da dimbin dukiya da kamfanonin boye a wasu kasashen da ba’a biyan haraji domin guje wa biyan harajin arzikin da suka mallaka ga gwamnatocin kasashensu.
Gidan Jaridar PREMIUM TIMES tare da wasu kamfanoni 100 ne suka gudanar da wannan bincike da kuma wallafa bayanai akan badakalar da irin wadannan shugabannin da jiga-jigan ‘yan kasuwa na duniya suke aikatawa.
An Karrama gidan Jaridar PREMIUM TIMES da kyauta mafi daukaka a aikin Jarida na kasar Amurka
A kasa Nigeria, Gidan Jaridar Premium Times ne kawai ta samu wannan dama na shiga dandalin da irin wadannan bayanai ‘Panama Papers’ suke a ajiye da kuma zakula su don wallafawa a jaridar ta.
Kamfanonin da suka gudanar da wadannan bincike sun yi ne a inuwar Kungiyar ‘International Consortium of Investigative Journalists’ wanda ya hada da shahararriyar gidan jaridar kasar jamus dinnan mai suna Suddeutsche Zeitung, da wasu gidajen jaridu 100 a duniyar mu.
Karanta labarin a shafin mu na Turanci a nan: Celebrations at PREMIUM TIMES as Panama Papers wins Pulitzer Prize