Duk da fama da rashin samun nasara a wasanni da kungiyar Arsenal take ta fama dashi, yau dai ta karya wannan kwarin domin ta doke takwaranta ta Leicester City da ci daya mai ban haushi.
Abin da kamar ba ayi ba, cikin minti na 86 Robert Huth ya ci kansu in da hakan ya sa Arsenal ta shiga gabansu da ci daya ba ko mai.
A sauran wasannin kuma, Spurs sun doke Crystal Palace da ci daya babu komai.
A kasar Spain kuma, Barcelona ta doke Osasuna da ci 7 da 1 in da Real Madrid ta doke Deportivo da 4 da 1.