Rundunar ‘yan sandan Najeriya sun karyata korafin da sanata Danjuma Goje yake ta yadawa kan wai sun tafi da takardun da ya kunshi bayanan kasafin kudin 2017 a farmakin da suka kai gidansa a makon da ya gabata.
Kakakin rundunar ‘yan sanda Moshood Jimoh ya karyata hakan in da ya ba da bayanai akan abubuwan da suka tafi da su.
Ya ce cikin abubuwan da suka tafi da su akwai takardu da ya shafi harkallar kasuwancin sa da na siyasa sannan akwai wasu takardu da ya ke tona yadda tsohon gwamnan jihar Kano Ibrahim Shekarau ya shirya yadda aka kashe Sheikh Ja’afar.
Ya ce ‘yan sandan sun sami takardar izinin shiga gidan Goje kafin su kai wannan farmaki.
“ Duk abin da muka yi a gidan Goje a gaban ‘yan uwansa mu kayi da ya hada da Aisha Umar, Danjuma Mohammed da Ango Usman kuma su ne suka bude mana gidan kuma suka kai mu daki daki a gidan.
“ Saboda karerayin da ake ta yadawa akan abubuwan da muka tafi dasu daga gidan Goje ya zama dole mu baku bayanai akan hakan.
Ga abubuwan da muka tafi dasu:
1 – Naira Miliyan ₦18,056,000
2 – Dala $19,850
3 – Riyal 9, 400
4 – Faloli 38 ciki akwai wanda aka bada bayanai yadda Ibrahim Shekarau ya shirya kashe Sheikh Ja’afar a Kano.
Moshood ya ce babu takarda ko da daya ne da ke da kowani irin bayanai akan kasafin kudin 2017.
Rundunar ta yi kira ga mutane da suyi watsi da abubuwan da Goje ya ke ta fadi akan farmakin da aka kai masa wai sun tafi da takardun da ke kunshe da bayanai akan Kasafin kudin 2017.