Ranar Alhamis din makon nan ne jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya su ka kai farmaki gidan tsohon gwamnan jihar Gombe Sanata Danjuma Goje.
Jami’an ‘yan sanda 25 ne da wadansu sanye da fararen kaya suka zagaye gidan sanatan a yammacin Alhamis din.
Hukumar EFCC ta sanar da cewa ba ita bace ta aika da jami’an ta gidan Goje, Umarni ne daga sifeton rundunar ‘yan sandan kasa Idris Ibrahim ga jami’an sa da su je gidan domin gudanar da bincike.
Bayan gudanar da bincike da akayi daki- daki a gidan an gano miliyoyin naira a wasu daga cikin dakunan da ke gidan.
Bayan haka kuma jami’an tsaro sun tafi da wadansu mahimman takardu.
Wani da ga cikin mai masa hidima ya shaida mana cewa jami’an ‘yan sanda basu nuna takardar bada izinin gudanar da bincike a gidan ba, sun fada ne kawai. Ya ce sunyi kaca-kaca da gidan kafin suka tafi a sanadiyyar binciken da su ka yi.
” Jami’an ‘yan sandan sai da sukayi awoyi hudu a cikin gidan suna bincike-bincike. Sun tafi da tsabar kudi da ya kai naira Miliyan 24, da ya hada da naira Miliyan 18, $19,000 da riyal din kasar Saudiyya na 4000.
“Idan ma wadannan kudade suka biyo to gaskiya ba’ ayi masa adalci ba domin mutum mai matsayi kamar na Goje ace wai babu irin wadannan kudade a ajiye a gidansa bayan irin mukaman da ya rike a kasarnan kuma dan siyasa ay ba zai yi ma’ana ba.
Koda yake shi Danjuma Goje bai ce komai ba akan abin da ya faru, kakakin rundunar ‘yan sanda Moshood Jimoh ya ce da zarar sun gama bincike akan musabbabin kai wannan farmaki gidan Sanata Goje za su sanar wa duniya.