TAMBAYA: Malam, don Allah ina so ka ba ni maganin sanko a Musulunci?
AMSA: Maganin sanko, akwai na Turawa. Sai ka je ka bincika.
TAMBAYA: Malam, mene ne hukuncin ’yan jaridar da ke yada hotuna marasa kyan gani masu tayar da hankali, kamar na cutar Ebola da sauransu? Shin akwai zunubi a cikin yada irin wadannan?
To, ai shi aikin jarida ya na da ka’idojinsa, ya na da dokokinsa. Don haka babbar inda matsalar ta ke kasancewa ita ce, hukumomi wanda a ka dora wa nauyin sa ido a kan abinda ya shafi dukkan wani abu na harkar jarida, su tabbatar da cewa a na bin abinda a ke cewa, (ka’idoji) da tsari na mutunci da kulawa a aikin jarida.
Don haka wadannan hukumomi su ne ya kamata mutane su rika caccakar su su ga cewa lallai sun tashi tsaye su ga cewa a na aiki da duk dokoki da ka’idoji na aikin jarida. To, wannan shi ne zai taimaki mutane. Shi dan Adam idan ya girma, wa’azi kadai ba su iya gyara rayuwarsa, sai an hada da dokoki ne zai iya gyarawa, saboda mafi yawan mutane tunaninsu da karfin zuciyarsu ba ya sa su su yi abinda ya ke daidai.
TAMBAYA: Malam, me ya sa wasu daga cikin malaman su na kyamar karanta littafin Mukhtaril Hadisin Nabawy na Sayyid Ahmad Alhashimy. To, shi ne na ke so na ji meye dalili?
To, ba kyamatar karanta shi ya kamata a yi ba saboda littafi ne da ya kunshi hadisan Annabi (SAW), to amma ka san a kan samu wasu mutane da su kan wuce gona da iri wajen yin abu, domin shi wannan littafi ya kunshi hadisai sahihai da kuma hadisai masu rauni matuka da gaske har ma da wasu hadisan da wasu malaman su ke ganin hadisan karya ne ko kuma marasa tushe ko marasa asali.
To, amma don cewa a littafi akwai hadisai da’ifai ko kuma akwai hadisan karya a ciki ko hadisai marasa tushe a ciki ko marasa asali, ba zai ba zai sa a kyamaci karanta wannan littafi ba, musamman saboda shi Mukhtaril Hadisin Nabawy littafi ne da a ka gina shi a kan tarbiyya da ilimi da kyakkyawar rayuwa, wato kamar a kira shi da suna General Studies ko General Knowledge ko a ce jakar magori cewa wacce za ta ba wa mutum komai da komai wanda za a sami tarbiyya.
Domin hatta su kansu hadisan da ba su da inganci a littafin za ka tarar su ma su na dauke da wata tarbiyya wacce za ta amfani mutum, domin sau da yawa hadisai ra’ifai, ba za a dogara da su a kan hukunci ba (wannan haka ne), ba kuma za a yi hujja da su a kan halak ko haram ba ko akida, amma sau da yawa za a ga cewa su na dauke da kyakkyawar ma’ana ta addinin Musulunci.
Saboda wasu lokutan za ka ga cewa irin wadannan zantuka, zantuka ne na mutanen kirki, na wasu salihan bayi, na wasu manyan mutane ko a sahabbai ko a tabi’ai, ko wasu malaman Musulunci ko wasu masu hikima da su ka yi bayani. To, wani kuma ko saboda rashin sani ko wani kuskure ko saboda kokarin abin ya zama karbabbe, sai ya jingina ga Annabi (SAW). Don haka littafin Mukhtaril Hadisin Nabawy, littafi ne mai kyau, amma ya na dauke da hadisai ra’ifai, marasa asali da kuma hadisan da a ka ce na karya ne, amma yawansu bai kai yawan wadanda su ke ingantattu a ciki ba.
Sannan kuma da ma littafi daga cikin Jami’al Sagir ya tarkato ya harhado ya kawo, sannan kuma littafi ne da a ka gina shi, domin tarbiyya, ba don hukunci ba, kuma wanda ya yi shi iya iliminsa ya yi da kyakkyawar zuciya. Akwai malamai da su ka yi aiki a kan littafin, su ka ware hadisai ra’ifai da kuma sahihai. Wasu kuma su ka fassara shi ma.
A cikin malaman da su ka fassara shi, akwai babban malamin nan na Kano, Marigayi Malam Nasiru Mustapha, wanda ya fassara shi da Hausa, kuma malamai da yawa sun yi ma sa ta’aliki na kokarin tace hadasan cikinsa da sauransu. Don haka bai kamata malami ya ce kada a karanta shi ba, sai dai ya ce, a karanta shi saboda tarbiyyar da ke ciki, amma a sami malamin da zai rika bayanin matsayin hadisan, don kada a yi hukunci da su.
Za ku iya tuntubar PREMIUM TIMES HAUSA ta hanyar turo tambayoyinku ta adireshin imel, hausa.premiumtimes@gmail.com da shafinfahimtafuska@yahoo.com da kuma https://www.facebook.com/premiumtimeshausa/