TAMBAYA: Malam, ya halasta na yi addu’a kan Allah Ya kashe ni, saboda talauci da halin kuncin da na ke ciki?
AMSA: To, na farko dai haramun ne ya roki Allah Ya kashe shi. Na biyu wajibi ne ya sami wani wanda zai ba shi shawarar yadda zai sami kyakkyawar rayuwa, saboda duk wahalar da ya ke sha Allah Ya sa ya rayu kuma ya na da wata baiwa da ni’ima wadanda ya ke bukatar wani ya tunasar da shi su. Annabi (SAW) ya hana mutum ya nemi Allah Ya kashe shi, saboda talauci ko saboda damuwa ko wani kangi da ya ke ciki. Kuma duk mutumin da ya nemi Allah Ya kashe shi saboda wata damuwa, to ya yi laifi, kuma kowacce irin masifa ko girman zunubi ya yi, bay a halasta ya kashe kansa ko ya ce Allah ya kashe shi ko ya nemi wani ya kashe shi. Wajibi ne ya sani cewa, Annabi (SAW) ya ce, mafi alherin mutane shi ne, wanda ya dade a duniya kuma ya yi aiki nagari.
TAMBAYA: Malam, mene ne maganin zinar hannu da na ke yawan yi, saboda har ta janyo mi ni raunin al’aura?
AMSA: To, akwai magani na Turawa da ya kamata ka je ka bincika a wajen likita. Sannan wajibi ne ka daina zinar hannu, domin za ta sabbaba ma ka mantuwa, ta raunana ma ka al’aura, sannan ta rikita ma ka lissafi da al’amuranka, kuma za ta raunana tunaninka ta cuci rayuwarka. Idan ba ka da ikon yin aure, ka sani cewa, ba kai kadai ne balagagge ba, ba ke kadai ce balagaggiya ba, ba kuma kadai ne ku ka fi kowa sha’awa ba. Akwai mutane da yawa da su ke da sha’awa, amma sun a daurewa. Don haka kai ma wajibi ne ka daure. Idan ki ka ji ko ka ji sha’awa ta dame ka ka yi tafiya mai yawa a kasa, ka daina kalle-kalle da sauraron duk wani abu da zai motsa ma ka sha’awa, ka kuma yawaita shiga cikin manyan mutane kuma ka daina yawan kadaita, sannan duk lokacin da sha’awa ta taso ma ka, ka sha ruwa da yawa, kuma sawa ranka cewa wannan abinda ka ke yi zai raunana ma ka mazakuta da kwakwalwa.
TAMBAYA: Malam, allura ta na karya azumi?
AMSA: A’a, allura ba ta karya azumi.
TAMBAYA: Malam, mene ne hukuncin mutumin da ya ke yin azumi, amma ba ya sallah?
AMSA: Azuminsa ya na nan, amma ya na da zunubin rashin yin sallah cikakkiya.
TAMBAYA: Malam, shekaruna 26 kuma Ina da sana’a, sannan Ina yin karatu. Ina tare da budurwata, amma iyayenmu sun ce ba za mu yi aure ba sai n agama makaranta. Ga shi kuma mu na bukatar juna. Ya za mu yi?
AMSA: Ka je ka samu wadanda mahaifanka su ke jin maganarsu kuma mahaifinka ya ke ganin girmansu ka nuna mu su cewa, ka na so su yiwa mahaifanka Magana su yard aka yi aure tunda ka na da sana’a kuma za ka cigaba da karatunka. Su kuma iyaye yakamata su gane cewa, bai kamata su rika hukunta ’ya’yansu da tunaninsu a kan abinda ya shafi sha’awa ba. Sau da yawa iyaye sun a samun zunubi, idan ’ya’ya su ka yi barna, saboda su ne bas a tsayawa su yi hukunci na gaskiya a kan ’ya’yansu su fahimce su, domin su a ganinsu su na ganin dole sai sun yi abinda su ke so, alhali ba sa ganin hakan ne ya ke sa su ke bude wa ’ya’yansu hanyar barna. Su kuma ’ya’yan su sani cewa, wannan ba dalili ba ne da zai sa su saba wa Allah mahalicinsu!
TAMBAYA: Malam, an tura ni karatu wata kasa a gidanmu, sai na je na dawo ban yi karatun ba. A dalilin haka mahaifiyata ta yi mi ni gori. Ni kuma sai na yi fushi na kwashe kayana na bar garin har ta tsufa ta na neman taimakona ban dawo ba. Yanzu abin ya na damu na. Shin ya zan yi?
AMSA: Ka roki Allah gafara, ka kuma roki mahaifiyar taka, domin kai ne mai laifi. An tura ka karatu, ba ka yi ba. Bai kamata da ya yi fushi da iyayensa ba.
Za ku iya tuntubar PREMIUM TIMES HAUSA ta hanyar turo tambayoyinku ta adireshin imel, hausa.premiumtimes@gmail.com da shafinfahimtafuska@yahoo.com da kuma https://www.facebook.com/premiumtimeshausa/