Alluran Rigakafin Sankarau kyauta ne – Gwamnati

0

Hukumar kula da kiwon lafiya na matakin farko NPHCDA ta sanar da cewa alluran rigakafin cutar Sankarau a Kasa Najeriya kyauta ne.

Shugaban hukumar Faisal Shuaib ne ya sanar da hakan yau a Abuja.

Yace sun sanar da hakanne ganin irin labaran da suka ta samu cewa wai wasu na biyan kudi kafin a yi musu alluran a asibitoci.

Shugaban hukumar ya kara da cewa gwamnatin Najeriya ta kashe kudade da dama domin ganin cewa ta wadatar da rigakafin alluran a fadin kasa Najeriya musamman jihohin da suke fama da cutar.

Ya roki mutane da su sanar da hukumar duk wanda ya bukaci kudi a hannun su kafin ayi musu rigakafin.
Yayi kira da a tsaftace muhalli sannan a rage yawan cinkoso a dakuna.

Share.

game da Author