Da safen Laraban nan ne Allah yayi wa shugaban kamfanin jiragen sama na Chancahangi Air, Alh. Ahmadu Chanchangi Rasuwa.
Allah ya dauki ran Alh. Ahmadu Chanchangi a hanyar su na zuwa asibiti a Abuja da safen yau.
Ya rasu ya na da mata uku da yaya 33. Daya daga cikin ‘ya’yan sa shine dan majalisa mai wakiltan Kaduna ta Kudu a Majalisar wakilai, Rufai Chanchangi.
Za’a yi jana’izan sa da karfe 2 na rana, a Kaduna.
Discussion about this post