Tsohon shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya zargi tsohon shugaban jam’iyyar PDP Adamu Mu’azu da yi masa Zagon Kasa a zaben 2015.
“ A rashin sani na ashe Adamu Mu’azu na yi wa jam’iyyar adawa na APC aiki ne a wancan lokacin ni ban sani.”
Jonathan yace idan ba cin amanar sa da wasu makusantarsa sukayi ba tayaya za’a ce wai ya fadi zabe a Jihohin Ondo, Filato da Benue.
“Wasu da muke tare da su sun shirya abin ne bamu sani ba domin idan ka duba yadda zaben ya gudana a wadannan jihohi, kusan duka masu zabe sunki fitowa su zabe mu saboda munafurta mu ada kayi.
Jonathan ya fadi hakan ne a wata littafi da ya rubuta wanda gidajen Jaridun The Nation da Cable suka dan tsakuto kadan daga ciki.
A cikin rubutun, Jonathan ya ce Buhari ya na ruguza duk abubuwan da ya gina a lokacin yana shugaban kasa.
“ Maimakon Buhari ya dora akan abinda na bari, ya zo yana ta bata shirin da nayi a wancan lokacin. Ya sa iyalai na a gaba a yakin sa na cin hanci da rashawa da yake yi.”
“ shi ma shugaban hukumar Zabe a wancan lokacin ya bani mamaki domin ya ci amanata. Har yanzu ban san dalilin sa na kikacewa wai dole sai anyi zabe a watan Fabrairu ba kafin mu amince a daga Zaben.