Kakakin shugaban Kasa Garba Shehu ya sanar da cewa babu maganan wai Abba Kyari da shugaban hukumar DSS Lawal Daura sun ajiye aikinsu karya ce kuma nabu irin wannan magana.
Garba Shehu ya ce wadannan maganganu da ake ta yadawa a kafafen yada labarai karerayi ne kawai.
“ Yanzu haka da ni ke Magana shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aiki Abba Kyari zuwa kasar China wanda muna sa ran dawowar sa a tsakiyar wannan makon. Shi kuma Lawal Daura na nan a ofishisa ya na ayyukansa.
Ya ce wadannan zantuttuka basu da asali sannan yayi kira ga mutane da suyi watsi da su.