A sanadiyyar farmakin da jami’an ‘yan sandan suka kai gidan Sanata Danjuma Goje, wanda shine Shugaban kwamitin kasafin kudin majalisar dattawa zai iya sa a jinkirta mika kasafin kudin da majalisar ta ke kokarin kammala aiki akai wanda Buhari ya mika tun a watan Disembar 2016.
Wani mai taimakawa sanata Goje ne ya sanar da mu hakan inda ya ce lallai za’a samu wannan matsalar domin jami’an tsaro sun tafi da wasu takardu masu yawa da ya kunshi wasu bayanan akan aikin kasafin kudi.
Buhari ya mika kasafin kudin 2017 tun a watan Disembar 2016 inda tun a wancan lokacin ake sa ran majalisa zata kammala aiki akai ta amince da kasafin.
A watan Fabrairu ne ake sa ran hakan kafin majalisar ta nemi karin lokaci zuwa watan Mayu.
Wannan samame da aka kai gidan Sanata Goje inda kuma muka ji wai an hada da wasu takardu na aikin kasafin kudin zai iya tsawaita aikin har ya wuce watan Mayu kamar yadda kwamitin ta ke kyautata zaton za ta kammala aiki a kai.
Ranar Alhamis din makon nan ne jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya su ka kai farmaki gidan tsohon gwamnan jihar Gombe Sanata Danjuma Goje.
Jami’an ‘yan sanda 25 ne da wadansu sanye da fararen kaya suka zagaye gidan sanatan a yammacin Alhamis din.
Bayan gudanar da bincike da akayi daki- daki a gidan an gano miliyoyin naira a wasu daga cikin dakunan da ke gidan.
Bayan haka kuma jami’an tsaro sun tafi da wadansu mahimman takardu.
Wani da ga cikin mai masa hidima ya shaida mana cewa jami’an ‘yan sandan basu nuna musu wani takardar neman izinin shiga gidan ba, sun fada ne kawai. Ya ce sunyi kaca-kaca da gidan kafin suka tafi a sanadiyyar binciken da su ka yi.
” Jami’an ‘yan sandan sai da sukayi awoyi hudu a cikin gidan suna bincike-bincike. Sun tafi da tsabar kudi da ya kai naira Miliyan 24, da ya hada da naira Miliyan 18, $19,000 da riyal din kasar Saudiyya na 4000.
“Idan ma wadannan kudade suka biyo to gaskiya ba’ ayi masa adalci ba domin mutum mai matsayi kamar na Goje ace wai babu irin wadannan kudade a ajiye a gidansa bayan irin mukaman da ya rike a kasarnan kuma dan siyasa ay ba zai yi ma’ana ba.
Koda yake shi Danjuma Goje bai ce komai ba akan abin da ya faru, kakakin rundunar ‘yan sanda Moshood Jimoh ya ce da zarar sun gama bincike akan musabbabin kai wannan farmaki gidan Sanata Goje za su sanar wa duniya.