Ikilisiyar ‘Omega Fire Ministries’ ta zargi gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’I da hunnu a zargin aikata fasikanci da ake yi wa faston ikilisiyan Johnson Suleman.
Kakakin ikilisiyar Phrank Shaibu ne ya fadi hakan ranar Talata akan wasu hujojin da ya ce suke da shi wanda ya nuna cewa gwamnan jihar Kaduna ne yak e wa gwamnan bita da kulli.
Ya ce gwamnan ya yi hakan ne domin ya ci mutuncin faston akan wata wasikar da ya rubuta wa gwamnan akan yadda gwamnan ya nuna halin ko in kula akan rikicin kudancin Kaduna.
Bayan haka Shaibu ya ce da farko sun yi watsi da wasikar wani mai suna Festus Keyamo inda yace El-Rufa’I ya dauki hayan wasu mutane domin su kwaikwayi muryar faston da kuma hada bidiyo akan shi Suleman din wai ya na aikata fasikanci.
Ya ce sun sami tabbacin hakan ne lokacin da wata mata mai suna Queen Esther ta kara tabbatar musu da cewa tabas gwaman jihar Kaduna ya dauki hayan wasu mutane domin su bata sunan Suleman.
Shaibu yace abinda gwamnan ya keyi domin bata sunan faston bai basu mamaki ba musamman ganin cewa hakan ya faru ne tun bayan lokacin da Suleman ya ce El-Rufai ba ya yin komai domin kawo karshen rikicin kudancin Kaduna.
Daga karshe ya yi kira ga jami’an tsaro da su binciki aiyukkan gwamnan.