Farfesa Mike Ogirima likita ne wanda ya kware a gyaran kashi da fidar cutar tabuwan hankali kuma shine shugaban kungiyar likitocin Najeriya.
Ogirima ya fadi irin illolin da aiki da likitocin da basu kwareba kan kawo ga mara lafiya.
Ya yi bayanin hakan ne a wata hiran da gidan jaridar PREMIUM TIMES ta yi da shi.
A bayanin da ya yi yace likitan da bai kware a aikin likitanci ba shine mutumin da bai sami isasshen karantawaba akan akin likitanci kuma yake duba marasa lafiya amma kwarraren likita shine wanda ya sami cikakkiyar karantarwa da kwarewa kan aikin likitanci domin kulawa da duba marasa lafiya.
Yace akan bude shagunan bada magani ba tare da samun amincewar kungiyar kula da ba da lasisi domin bude irin wadannan shaguna ba. Kuma irin wadannan masu shago sukan bada magunguna ga marasa lafiya ba tare da sun san asalin abun da yake damun wadannan masu ciwo ba saboda rashin kwarewa.
Bayan haka kuma ya koka da yadda wasu malaman kiwon lafiya suke rikidewa su zama likitocin dole musamman wadanda suke aiyuka a kauyuka.
Ya ce kungiyar likitocin Najeriya na kokarin ganin cewa duk likitocin da suke aiki a kasa Najeriya sun yi musu rajista da kungiyar sannan kuma ta baiwa kowane likita da ya yi rajista da kungiyar tambarin da zai taimaka wajen gano likitocin da ba su kware ba a aikinsu.