An yi wa Buhari Addu’a a Gaya, jihar Kano

0

A cigaba da addu’o’i da ake ta yi wa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadin kasannan musamman a Arewacin Najeriya,a karamar hukumar Gaya da ke jihar Kano an gudanar da irin hakan.

Mai taimaka wa Shugaban Kasa akan sababbin kafafen yada labarai Bashir Ahmed ya halarci taron yin addu’o’in.

An karanta Kur’ani mai girma da yin addu’o’i ga shugaban kasa.

An gudanar da irin wadannan addu’o’i a jihohin Kebbi, Bauchi, da jihar Kano.

A jihar Kaduna ma za’a yi irin wannan addu’o’i inda sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad zai halarta ranar Lahadi.

Share.

game da Author