Shugaban ‘yan canji masu rijista na kasa Aminu Gwadabe yace a dalilin hubbasan da gwamnati ta keyi na wadata kasa Najeriya da isasshen dala ‘ yan canji sun yi hasaran naira miliyan 130 a cikin mako daya.
Aminu Gwadabe ya ce mutane sun ki siyan dala a kasuwan bayan fagen wanda hakan ya sa ciniki ya Karanta.
Gwadabe ya jinjina wa gwamnati da irin wannan himma da takeyi domin Kawo karshen tashin gwauron zabin da dalan takeyi a kwanakin baya.
Yace kungiyar sa zata ci gaba da marawa gwamnati baya akan hakan sannan yayi kira ga jami’an tsaro da su sa ido domin kau da baragurbi a cikinsu wanda ke yin aikin canjin a iyakokin Najeriya.
Discussion about this post