Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya Kwamared Shehu Sani yace yakin basasar da ake yi tsakanin ‘yan gaban goshin Buhari ne ya hadiye Ibrahim Magu.
Shehu Sani yayi Kira ga shugaban kasa da ya maida hankalin sa sosai akan abinda yakeyi idan ba haka ba wadannan mutane zasu ruguza masa gwamnati.
Ya Kara da cewa Buhari shi kadai ba zai iya yaki da cin hanci da rashawa ba bayan na jikinsa duk suna da guntun kashi a duwawunsu.
Ya ce kowa ya sani cewa bayan shugaban kasa da mataimaki sa toh sai kuma shi ne kawai suka fadi ma duniya abun da suka mallaka kafin su hau kujerun mulki suran duk sun ki sanar da duniya hakan.
Ya fadi hakan ne da ya ke tattaunawa da kungiyar dalibai lauyoyi musulmai na kasa a ofishinsa a ziyarar ban girma da suka kai masa.
Idan ba’a manta ba wata kwamitin majalisar dattijai wanda shi Sanata Shehu Sani ya shugabanta ta kama sakataren gwamnatin tarayya da hannu dumu-dumu a badakalar kwangilar cire ciyawa a kogin Yobe amma daga baya shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karyata rahoton kwamitin duk da ga shi karara binciken ya nuna cewa ba’ayi gaskiya ba a aikin da akayi kuma ya nuna irin kudaden da shi sakataren gwamnatin tarayya ya waske da su a dalilin hakan.