Sanata mai wakiltan Kaduna ta Tsakiya Kwamared Shehu Sani ya ce lallai ya kamata jam’iyyar su ta APC ta hukunta gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai saboda wasikar da ya rubuta wa Buhari sannan kuma ya mika wa gidanen jaridu domin su wallafa a boye.
Sanata Sani ya ce tayaya za’ace wai mutumin da baya kaunar a yi masa adawa kan aiyukansa ace wai har shine zai yi ma wani.
Ya ce tunda ya harba makamansa na adawa akan shugaban kasa Muhammadu Buhari, lallai shima ko dole ayi masa raddi akan hakan kuma ayi masa adawa.
” Ya zargeni da yi wa Buhari cin fuska domin na fadi gaskiya ta a wancan lokacin sai gashi yanzu da kansa ya ke ci wa Buhari da jam’iyyar su ta APC mutunci da sunan rubuta wasika zuwa ga shugaban kasa sannan ya zagaya ya mika wa ‘yan jaridu domin su yada abun.
“Banbancin nawa adawar da nashi shine no na kan fito ne karara in fadi abinda ya kamata ayi amma na El-Rufai kuwa a munafince ya keyin nasa.
“El-Rufai yayi hakan ne domin mutane su ga kamar abin kirkine yayi domin share fagen neman zama magajin Buhari amma ba da wata manufar gaske yayi ba.