Ya kamata a dawo da karantar da Arabi a makarantun mu – Inji Sarkin Kano

0

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ya yi kira da a dawo da karantar da darasin Arabi a makarantun kasa Najeriya.

Sarkin yayi kiran ne a taron lekcan tunawa da Thomas Hodgin da kayi Jami’ar Oxford da ke kasar Ingila.

Sarki Sanusi yace koyar da darussan Arabi a makarantun kasa Najeriya zai taimaka wajen gyara dabiun mutane musamman yara ‘yan makaranta.

Ya koka da yadda ake nuna ma wadanda suke da ilimi na Arabi bambamci da yi musu izgilancin cewa wai tunda basuyi karatun Boko ba, ba masu ilimi bane.

Daga karshe ya yi kira da a kula da yadda ake bada auratayyar ‘yan mata kanana tun basu balaga ba a wasu kasashen duniya.

Yace ya kamata ayi koyi da kasar Amurka wajen hana aurar da ‘yarinyar da bata kai ayi mata aure ba.

Tsohon shugaban hukumar Zabe ta kasa, Attahiru Jega na daga cikin wadanda suka halarci taron.

Share.

game da Author