WATA SABUWA: Mata sun ce takalma masu tsini na rufa musu asiri wajen boye gajartarsu duk da matsalolin dake tattare da saka su

1

Mafi yawan mata na sha’awar musamman a wanna karni sun karkata da yin ado da takalma masu tsini.

Wasu mazaje da yawa sukan nuna bacin ransu ga matansu ko kuma budurwansu musamman idan suka ga basa yi musu ado da irin wadannan takalma.

Sai dai kash, ga dadi ga wuya domin bincike da masana sukayi akan saka irin wadanna takalma ya nuna cewa takalman na kawo matsala ga kashin baya da jijiyoyin masu amfani da su.

Gidan jaridar PREMIUM TIMES HAUSA ta yi bincike akan ko mata za su iya rabuwa da yin amfani da takalma masu tsini ko da sun san irin illolin dake tattare da saka irin wadannan takalama.

A wata hiran da wannan gidan jaridar ta yi da wani likita a Makurdi mai suna Martins Adejo ya gargadi mata da su yi taka tsantsan da saka takalma masu tsini domin ya na lahanta kashin bayan mutum kamar su ciwon baya, raunana kashi da sauransu.
Ga yadda tattaunawar da wadansu mata ta kaya akan saka irin wadannan takalma.

Maimuna Kabuk ta ce tabas tana da masaniya cewa saka takalmi mai tsini na da illoli sosai a jikin mace domin yakan samarda ciwon baya, za a iya turgudewa wanda yakan kawo targde ko kuma gocewan kashi.

Ta kuma ce akwai lokacin da ta kusa samun targade ta dalinlin saka takalmin amma har yanzu ba ta daina saka suba saboda aikin da take yi ya bukaci ta saka.

Bilkisu Ahmed ta ce ta san cewa saka takalman nada illa a jiki amma sai dai idan mace na saka su kullum ne shine za ta sami irin wannan matsalar saboda ta ce tana saka takalman amma ba kullum ba domin a gaskiya tana sha’awar sa su.

Ita kuma Rahoofat ta ce a na ta ra’ayin idan mace na saka takalman da ake kira ‘’Block Heels’’ ba za su kawo mata irin wadannan illoli da ake Magana akai ba amma sauran takalman masu tsini da ba wadannan ba suna kawo illoli saboda hakan ya sa take saka irin wadannan da ta Ambato a baya.

Zainab Dariya ta ce kodaye ke tana da tsawo kuma ta san illar da wadannan takalman ke kawowa duk da hakan tana saka su musamman lokacin buki ko sha’ani.

Amina Yusufu Dan Ali ta ce dama can it aba ma’abuciyar irin wadannan takalma bane. Ba ta sha’awar saka irin wadannan takalman saboda irin illolin da ta ga yake kawo wa.

Rahila Barnabas ta ce a ra’ayin ta mata ba za su daina saka takalmi masu tsini ba domin yana rufa wa marasa tsawo asiri, yana kara musu dan kwarjini a ado.

A takaice dai takalmi mai tsinin ya na matsaloli kuma yana nashi fito da ‘ya mace musamman idan ‘yar gayu ce. A dalilin hakan ya sa komai tsadar takalman mata ke rubibin siya.

Share.

game da Author