Kotu a jihar Kano ta daure wani magidanci kuma dan kasuwa mai suna Lawan Zubairu saboda aikata fyade akan wasu ‘yan biyu ‘yan shekaru 11.
Dan sandan da ya shigar da karan Rufa’I Inusa yace mahaifin ‘yan biyun Ibrahim Musa wanda ke zama a Hotoron Fulani Quarters a jihar Kano ne ya shigar da karar ranar 18 ga watan Maris.
Ya fadi wa kotu cewa Zubairu ya rudi yaran ne da su bishi zuwa gidansa in da daga nan ya danne su yayi musu fyade.
Shi Zubairu da ake zargi da aikata wannan mummunar aiki ya ki amincewa da zargin.
Alkali Muhammad Jibril ya yanke hukuncin da a daure shi har sai bayan ya yi shawara da babbar Darektan hukumar kula da irin wannan laifuka na jihar Kano sannan kuma ya daga ci gaba da sauraren karan zuwa 27 ga watan Afirilu.