UNICEF za ta kara yawan tallafin da take badawa a jihar Barno

0

Asusun tallafawa yara na majalisar dinkin duniya UNICEF ta sanar da cewa yara 50,000 ne a jihar Barno ke fama da matsalar yunwa sannan suna bukatar Kula ta musamman a bangaren kiwon lafiyar su.

UNICEF ta ce dalilin haka ya sa za ta kara yawan tallafin da take badawa.

Wani babban darekta a hukumar Omar Abdi ya fada wa gidan jaridar PREMIUM TIMES cewa ba abin mamaki ba ne yadda mutanen jihar Barno ke fama da matsalar yunwa da bukatan kiwon lafiya saboda yadda jihar ta yi fama da aiyukkan Boko Haram wanda hakan ya sa hukumar take tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fannin domin ci gaba da ba agaji a jihar.

Share.

game da Author