Asusun tallafawa mutane na majalisar dinkin duniya (UNFPA) ta ce kasa Najeriya za ta iya samun biliyan 1.5 idan har tana yin zubi da tanaji a kiwon lafiyar uwaye mata.
Wani ma’aikacin hukumar Eugene Kongnyuy ne ya fadi hakan ranar Laraba a taron kaddamar da jakadan kiwon lafiyar uwaye mata na yammacin Afrika da na Afrika ta tsakiya.
Kongnyuy ya yi bayanin cewa idan aka yi jimlar adadin yawan matan da ke mutuwa gaba daya a duniya za a ga cewa ana hasaran biliyan 15 kowane shekara amma idan aka yi zubin dala daya misali a kiwon lafiyar uwaye mata za a sami ribar dala 120.
Ya kuma kara da cewa yanzu ne ya kamata a dauki mataki kan samar da kiwon lafiyar uwaye mata wanda rashin hakan zai kawo koma bayan tattalin arziki,talauci, rashin cigaban kasa da sauran su.
Kongnyuy ya ce duk da cewa nauyin kiwon lafiyar uwaye mata ya rata ya akan gwamnati duk da haka hukumar na bukatar hadin kan kungiyoyi, masu ruwa da tsakin malamai da dai sauran su domin shawo kan matsalar.
Ya ce a yanzu haka kashi 55 bisa 100 na mata masu dauke da juna biyu na haihuwa ba tare da taimakon unguwar zoma ba ko wata ma’aikaciyar kiwon lafiya sannan kuma kashi 12 bisa 100 daga cikin su ne kawai ke samun ingantacciyar kulan da masu dauke da juna biyu ke bukata.
Kongnyuy y ace koda yake sun samu nasarori akan hakan har yanzu akwai aiki mai yawan gaske da ya kamata a yi wanda ya shafi wayar da kan mutane da daukan matakain da ya kamata domin a kawo karshen wadannan wahalhalu.