An tura Jami’an ‘yan sanda 350 zuwa titin Abuja zuwa Kaduna

0

Rundunar ‘yan sandan Kasa ta sanar da tura jami’an ta 350 zuwa babban titin Kaduna zuwa Abuja domin samar da tsaro.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Neja Muazu Zubairu ya ce an tura jami’an tsaron ne saboda a samar da cikakken tsaro ga matafiya a hanyar.

Kwamishinan ya ce an wadata jami’an da kayan aiki domin samar da cikakken tsaro a titin.

Yace wannan hadin gwiwa zai samu ne daga rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna da na Abuja.

A makonnan ne wasu ‘yan bindiga sukayi garkuwa da wadansu matafiya a titin da ya biyu ta garin Bwari inda suka sace mutane biyu daga cikin matafiyan.

An ce barayin sun bukaci a basu naira Miliyan 10 kafin su saki mutanen.

Share.

game da Author