Gwamnan jihar Barno Kashim Shettima da wadansu sarakuna da shugabannin siyasa daga jihar Barno sun ziyarci shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki domin neman sulhunta tsakanin Saraki da Sanata Ali Ndume.
Shettima ya jagoranci sarakunan ne da shugabannin siyasa daga jihar ranar Barno ranar Alhamis.
Tawagar na neman ganin an janye dakatar da Ali Ndume da majalisar tayi ne har na wata shida.
Bayan haka kuma za su gana da wadansu daga cikin shugabannin majalisar kamar yadda majiyar mu ta sanar da mu.
Majalisar dattijai ta dakatar da tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar ranar Larabar da ya gabata.
Majalisar ta dakatar da Ndume ne saboda wai shine ya nemi majalisar da ta binciki badakalar siyan motar da ake zargin shugaban majalisar Bukola Saraki da siya ba tare da takardu na ainihi ba da kuma zargin cewa wai sanata Dino Melaye bai gama karatun jami’a ba.
Kwamitin da ta mika sakamakon bincikenta yau a zauren majalisar ta ce sanata Ndume ya yiwa majalisar karya.
Kwamitin ta ba da shawarar a dakatar da Ali Ndume na shekara daya, in da bayan haka majalisar ta amince da dakatar dashi na wata shida.
A makon da ya gabata Sanata Ndume ya tashi a zauren majalisar domin sanar wa majalisar cewa ya karanta rahotanni a jaridu cewa wai Shugaban Majalisar dattijai Bukola Saraki yana da hannu a wata badakalar shigo da wasu motoci ba tare da takardu na gaskiya ba. Ya kara da cewa kuma akwai wasu rahotanni duk da haka akan sanata Dino Melaye akan wai bai kammala karatunsa na jami’a ba.
Ya mika shaidan abubuwan da ya karanta da inda ya karantasu a gaban majalisar.
A dalilin haka majalisar ta umurci kwamitin ta na da’a da ta gudanar da bincike akan hakan sannan ta mika mata sakamakon binciken.
Bayan wannan bincike da kwamitin ta gudanar wanda ta gaiyaci shugaban jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria da kuma dilolin da suka shigo da motar da ake Magana a kai duk sun bada bayanansu kwamitin ta wanke shugaban majalisar da Sanata Dino Melaye.
A zaman ta na majalisar ta amince da dakatar da Ali Ndume akan wai bayanan da ya bayar a wancan lokacin da yayi sanadiyyar yin bincike akan korafe-korafen duk karya ne.