Sanin kowa ne cewa tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai Ali Ndume kwararren dan majalisa wanda ya goge a harkar ayyukan majalisa.
Bayan irin goyon bayan da ya nuna ma shugaban majalisar Bukola Saraki a lokacin da yake neman kujeran shugabancin majalisar dattijai din ya saka bakin tabarau domin nuna rashin mutuncinsa karara ga duk wanda ya yi adawa da wannan shiri nasu.
Bayan sun samu nasarar hakan, Ali Ndume ya fara samun matsala ne da shugaban majalisar tun bayan nuna goyon bayan sa da yayi karara ga neman amincewar majalisar da ta tabbatar wa Ibrahim Magu da kujeran shugabancin hukumar EFCC.
Ndume yayi kokarin ganin hakan ya yiwu amma har yanzu ana ta kai ruwa rana akan maganar Ibrahim Magu din.
Hakan ya sa shugabannin majalisar basu gamsu da biyyarsa ba kuma kwatsam sai a ka tsigeshi daga kujeran shugaban masu rinjaye na majalisar dattijai aka nada Ahmad Lawan wanda da shine zabin jam’iyyar.
A makon da ya gabata Sanata Ndume ya tashi a zauren majalisar domin sanar wa majalisar cewa ya karanta rahotanni a jaridu cewa wai Shugaban Majalisar dattijai Bukola Saraki yana da hannu a wata badakalar shigo da wasu motoci ba tare da takardu na gaskiya ba. Ya kara da cewa kuma akwai wasu rahotanni duk da haka akan sanata Dino Melaye akan wai bai kammala karatunsa na jami’a ba.
Ya mika shaidan abubuwan da ya karanta da inda ya karantasu a gaban majalisar.
A dalilin haka majalisar ta umurci kwamitin ta na da’a da ta gudanar da bincike akan hakan sannan ta mika mata sakamakon binciken.
Bayan wannan bincike da kwamitin ta gudanar wanda ta gaiyaci shugaban jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria da kuma dilolin da suka shigo da motar da ake Magana a kai duk sun bada bayanansu kwamitin ta wanke shugaban majalisar da Sanata Dino Melaye.
A zaman ta na yau majalisar ta amince da dakatar da Ali Ndume akan wai bayanan da ya bayar a wancan lokacin da yayi sanadiyyar yin bincike akan korafe-korafen duk karya ne.
Abin tambaya anan shine shi Ali Ndume ne yayi karya koko jaridun da yace sun rubuta maganganun ne sukayai karya?
Dakatar dashi dai ya nuna irin karfin da shugaban majalisar dattijai yake da shi wajen tankwasa duk wanda yaso a majalisar ko ana so ko ba’a so.