Tsakanin Hameed Ali da Sanatoci: Ba’a nada ni shugaban Kwastam don saka Unifom ba

2

Shugaban hukumar Kwastan Hameed Ali ya ce ba an nada shi shugaban hukumar kwastam bane don ya dunga saka Uniform.

Majalisar Dattijai sun bukaci Hameed Ali da ya zo gabanta domin amsa wadansu tambayoyi kan tilastawa masu shigo da motoci ta iyakokin Najeriya da yin rijista da hukumar da kuma wadansu abubuwan da hukumar ta keyi da bai gamsar dasu ba.

Hameed Ali yace an nada shi ne domin yayi aiki ba yawo da Unifom ba.

Shugaban hukumar kwastam din ya fadi hakanne a wata hira da yayi da gidan talabijin na TVC inda ya maida wa majalisar Dattijai martini kan gaiyatarsa da sukayi da yazo gabanta amma fa sanye da Uniform din Kwastam.

Yace abinda ya kamata su majalisar su matsa domin sani shine irin aiyuka da nasararin da ake samu a hukumar tun bayan ya zama shugaban hukumar ba saka unifom ba.

Yace baya tsoron fuskantarsu amma fa hakan zai yiwu ne idan aka samu jitua da fahimtar juna a tsakaninsu.

“ Abin da ya kamata su sa ido akai shine, shin ina yin aikin ko A’a.”

“Har yanzu ban ga takardan gaiyatarsu baa mm idan har suka bi ta hanyar da ya kamata, wato hanyar da ake bi domin gaiyatar jami’in gwamnati, tabbas zan amsa gaiyatar.”

Share.

game da Author

  • Alhamdulillah muna kara godewa Allah da ya kawo muna baba buhari gida lafiya Allah ya kara maka lafiya

  • A.Ahmad

    Kwarai kuwa aikin ka ya kamata su duba, shin kana aiwatarwa yanda ya dacene ko kuma a’a, bawai suyi ta barazana ba. Domin mun riga mun san su, kuma kansu kawai sukewa aiki ba Al’umma ba.