Wani tsohon janar a sojin Najeriya David Jemibewon, ya ce da shine majalisa ta bukaci ya saka Unifom din kwastam da sai dai ya ajiye aikin.
Janar David yace bai ga dalilin da zai sa wai ace maganar saka riga ya zama abin tada hankali ba.
” Ai nuna kaskanci ne ace wai tsohon soja da ya rike matsayi irin na Hameed Ali ya saka unifom irin na kwastam.
“Babu wani Wanda ya isa ya tilastani saka unifom a matsayina na tsohon janar a sojin Najeriya. Da inyi haka gara in ajiye aikin.
“Hameed Ali mutumin ne wanda ya yi aiki da samun yabo masu yawa a aikinsa. Ya koma ya saka kayan kwastam kuma ai ci baya ne.
Tsohon ministan sufurin jiragen sama Femi Fani Kayode ya musanta korafin Janar David in da ya ce ana shi ganin dole ne a Hameed Ali ya saka unifom kuma idan yaki a Kawo shi majalisa ko da cikin sarka ne zuwa majalisar