Mataimakin Darektan hudda da jama’a na sojin Najeriya Kingsley Umoh ya musanta zargin da wasu kafofin yada labarai suka yi akan su cewa wai sun kashe makiyaya 17 a kudancin jihar Kaduna.
Ya fadi hakan ne a Kaduna inda ya yi bayanin cewa babu gaskiya a zargin.
Umoh yace gwamnati ta turo su ne domin samar da zaman lafiya a yankin kuma a duk tsawon zamansu sun sami hadin kai da kyakkyawar mu’amula da sarakuna yankin, kungiyar Miyetti Allah da kuma masu fada aji a yankin.
Ya kuma shawarci mutane musamman masu fada aji a yankin da shugaban al’umman da su kwabi mutane akan yada jita-jita domin hakan hakan zai dagula nasarar samar da tsaro da aka samu zuwa yanzu a yankin.
Ya ce a ranakun 19 zuwa 22 na watan Maris din da muke ciki rundunar sojin ta sami nasaran kama wasu ‘yan ta’adda guda 4 sannan sun kashe 2 kuma akwai wasu biyu da suke daure a hannun jami’an tsaro.
Daga karshe ya ce sojojin sun ci gaba da aikin duba gari dare da rana a hanya da kewayen Gidan-Waya-Jagindi da Asso.