Shugaban Kasa Muhammadu Buhari yau ya mika wasikar dawowa aiki bayan kwananki 51 da yayi baya kasa Najeriya.
Buhari ya rubuta wasikar dawowarsa aikine zuwa ga shugabannin majalisar dattijai da na wakilai na kasa.
Buhari ya dawo kasa Najeriya ne ranar Juma’a.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika godiyarsa ga ‘yan Najeriya kan addu’o’i da suka yi ta yi masa tun da ya bar kasa zuwa kasar Ingila domin duba lafiyarsa.
Buhari ya fadi hakanne a lokacin da ya ganawa da jami’an gwamnati a fadar shugaban kasa jim kadan bayan ya dawo daga kasar Ingila.
‘’Na gode da addu’o’in da Musulmai da Kiristoci su ka yi ta yi mini.
‘’Hakan ya nuna cewa duk da wahalhalun da kasa Najeriya ta ke fama da shi mutanen Najeriya tare da gwamnati kai da kafa.
Buhari ya kara da cewa ya sami sami sauki sosai domin irin kulan da likitoci suka bashi a tsawon zaman sa a kasar Britaniya.