Buhari ya fadi hakanne a shafinsa na sadarwa ta twitter in da yace Faston ya kawo masa ziyara ce domin mika gaisuwarsa da kuma duba shi.
Bayan haka kuma shi kansa Justin Welby din ya rubuta hakan inda ya saka hotunan ziyarar nasa a shafinsa na twitter.
Buhari ya na kasar Ingila domin yin hutu da ganin likitocinsa kan lafiyarsa.
Ana gudanar da addo’o’I a masallatai a fadin kasa Najeriya domin nema ma shugaban kasa Muhammadu Buhari lafiya.
A Makon da ya gabata kuma Buhari ya kira tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da gwamnan jihar Kogi domin taya Obasanjo murnan zagayowar ranar haihuwarsa.