Sarki Sanusi ya yi kira da a dunga nada kwararru a ma’aikatun gwamnati

0

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi yace rarraba mukaman gwamnati da akeyi bai kamata ace wai sai dole kowa daga kowani yanki na kasar nan ya samu ba.

Sarki Sanusi yace ya kamata a dunga ba mutanen da suka cancanta ne koda ba daga yankin da ya kamata a nada su bane.

Sarki Sanusi ya fadi hakanne a wata taron wayar da kai mai suna “The Role of the Legal Profession in Nation Building: the Nigerian Context.”

Mai martaban wanda shine shugaban taron, ya ce mai makon a maida hankali wajen faranta wa kowa rai kan raba mukamai musamman na irin ofisoshin da yake bukatar kwarewa, a zabo wadanda suka cancantane ya fi.

Ya ce a nada mutanen da suka cancanta yafi akan bin son rai wanda ya hada da yi ko dan burge addini ko don nuna kabilanci.

Game da cin mutuncin yara da akeyi kuma sarki Sanusi yace “ Babu wata addini da ta halatta cin mutuncin yara kanana. Za ka ga yara kanana a titunan garuruwan mu suna tallace-tallace mai makon ace suna makaranta ne.

Sannan yayi kira ga iyaye da su yi shawara da ‘ya’yansu mata kafin su aura musu mazajen aure.”

Share.

game da Author