Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Sokoto Balarabe Kakale yace cutar Sankarau ya yi sanadiyyar mutuwan mutane 21 a kananan hukumomi 7 na jihar.
Kananan hukumomin sun hada da Kebbe, Bodinga, Rabah, Wamakko, Gada, Dange/Shuni da Tureta.
Kakale yace tun bayan bullowar annobar gwamnati ta aika da likitoci 150, magunguna da kuma sauran kayayyakin aiki domin kulawa da mutanen kananan hukumomin dake jihar musamman wadanda suke fama da cutar da kuma kokarin rage yaduwar cutar.
Bayan haka kuma ana ta kokarin wayar da kan mutane akan yadda zasu kula da kuma kare kansu daga kamuwa da ga cutar sankarau a fadin jihar.
Ya kuma kara da cewa cutar ya kara yawa ne a jihar bayan wadansu dauke da ita sun shiga jihar daga jihar Kebbi.
Ya kuma koka da yadda mutane ke kin zuwa asibiti idan an kamu da cutar sais u dinga jingina ta da jifane ko kuma tsafi ne aka yi musu.
Daga karshe kwamishinan ya shawarci mutane akan kula da kansu domin samun kariya daga cutar wanda hakan zai kuma taimaka wajen kawo karshen cutar.