Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya Kwamared Shehu Sani yayi kira da a fara karantar da tarihin yadda turawa sukayi mulkin mallaka, ciniki da bautar bayi a makarantun kasa Najeriya.
Ya fadi hakan ne lokacin da ya ziyarci wasu wuraren tarihin cinikayyar bayi dake Badagry a jihar Legas.
Sanata Shehu yace kamata ya yi a fara karantar da daliban makarantun firamari da sakandare tarihin yadda akayi bautar bayi a nahiyar Afrika.
Sanata Shehu Sani ya mika wata kudiri domin zama doka don ta taimaka wajen gyarawa da kuma kare wuraren tarihin kasa Najeriya wanda daga hakan idan har ta samu amincewar majalisar zata zamo wata hanyar samun kudaden shiga a kasa Najeriya.
A yanzu haka majalisar na duba kudiri.
Ya yi bayanin cewa amincewa da wannan kudiri zai zama wata hanyar da zai taimaka wurin bukasa koma bayan tatalin arzikin da kasan ke fama da shi sannan kuma ya kare wuraren tarihin daga lalacewa saboda gaba.
Daya daga cikin ma’aikatan gidan tarihin bayi na Badagry Peter Mesewaku ya yi murna ziyarar da sanata Sani ya kai musu domin a ganinsa hakan zai taimaka wa sanatan da majalisar kasa wajen yanke shawarar daya kamata don samar da kariya ga wuraren tarihin kasa Najeriya.
Ya kuma ce gwamnatin jihar Legas na bada nata gudunmawar domin ganin cewa gidan tarihin ba ta lalace ba amma kamata ya yi gwamnatin tarayya ta taimaka itama ko don irin dinbin kudaden da za’a iya samu na shiga a ta dalilin hakan.
Sanata Sani ya ziyarci wuraren tarihi kamar su Dutsen Kufena, gidan tarihin cinikin bayi dake Badagry inda ya ga wurin da bayi suka sharuwa, gidan benen da aka fara ginawa a shekarar 1845, gidan da Ajayi Crowther ya zauma da kuma sauran su.