Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce sai da ya shekara biyu da rabi yana rokon shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi takaran shugaban cin kasa a 2015.
El-Rufai ya fadin hakanne a wata hira da yayi da gidan jaridar Daily Trust na ranar Lahadi.
“Sai da na shekara biyu da Rabi ina rokon Buhari ya yarda ya yi takara a 2015 kuma shi da kansa ya fadi hakan ga kowa da kowa.
“ Ina da yakinin cewa samun nasarar kasar nan zai yiwu ne idan har muka yi hakan zagaye da Buhari a matsayin shugaba.
“Haryanzu ina wa shugaban kasa Muhammadu Buhari godiya saboda irin nuna amincewa da yayi da ni duk da bita da kulle da ake yi mini a wajensa.
El-Rufai yace daya daga cikin dalilan da ya sa ake yi masa irin wannan su ka kuwa shine kawai saboda ganin kusancinsa da Buhari da kuma yadda ya toshe kunnensa idan dai Magana ba don nasarar Buhari bace. Y ace wadannan abubuwa duk siyasa ce kawai ba wani abu ba.
“Abinda ya sa suke yi mani zagon kasa saboda sun san ni ainihin masoyin Buhari ne kuma sun tabbatar da cewa idan Buhari yace zai yi takara a 2019 ni ne zan zamo a akan gaba wajen yi masa kamfen haka kuma sun sani cewa idan ma yace bazai yi takara a 2019 toh duk wanda ya tsayar shine zan yi wa kamfen shine yasa suke so suga baya na.
Da aka tambayeshi akan kusantanshi da Abba Kyari El-Rufai yace Abba Kyari abokinsa ne kwarai da gaske.
“Ni da Abba Kyari abokanai ne amma kuma ya kamata kowa ya sani cewa bai san komai ba game da jam’iyyar APC, bashi da hannu a kafa ta haka kuma bai san yadda aka shirya sannan aka gudanar da kamfen din shugaban kasa ba. Wannan gaskiya ce na fada.
“Nace akwai wadanda sukayi bauta sannan sukayi aiki a kamfen din shugaban kasa amma an yi watsi dasu ana yi wa wadanda basu san komai ba.
“Na san Abba Kyari ba zai ki amincewa da abubuwan da na rubuta wa shugaban kasa ba. Yasan cewa hakan gaskice kuma ba a wasika ta bace ya fara jin hakan.