Bayan rundunar sojin Najeriya ta gama bincikenta akan dalilan da ya sa sojan ta Umaru ya aikata kisa ta mika shi gaban ‘yan sanda domin shigar da maganar a kotu.
Sunday Umaru yana da aure da ‘ya’ya.
A binciken da ‘yan sanda suka yi, Umaru ya furuta da bakinsa cewa buduwarsa Charity ta mutune bayan sabanin da suka samu a lokacin da ta ziyarce shi.
Wanda ya shigar da karar a madadin ma’aikatar Shari’a na jihar Filato Mr Awe yace sabanin ya auku ne lokacin da wayar budurwar Umaru Charity ya buga sai shi Saurayin nata ya dauka domin jin wanene yake kiran budurwar nasa.
Amsawar sa ke da wuya sai yaji muryar namiji ne kuma yana bukatar ya yi Magana da Charity.
Duk da cewa Umaru ya yi kokarin ya san wanene ke magana amma mutumin ya ki fada masa.
Daga nan ne fa sai Umaru ya je ya samu Charity a dakin girki sai ya tambaye ta wanene mutumin da ya kira ta a waya yanzu, ita kuma sai taki fada masa ko wanene.
Da musun yaki ci yaki cinye wa sai Charity tace ta hakura da soyayyar haka nan.
Umaru ya fusata bayan jin hakan sai ya wanke ta da mare ta ita kuma Charity dama can tana rike da wuka sai ta caka ma kanta a ciki.
Da ganin hakan sai Umaru ya zare wukar daga cikin ta ya yi mata yankar rago domin ya karusa ta kawai sannan ya jefar da gangan jikin nata a waje.
Da safe ya yi sai ya tafi wajen aikin sa inda ya nemi izinin shugabansa domin ya je ya ga iyalinsa .
Awe yace mazauna unguwan ne suka tsinci gawar Charity sannan suka sanar da hukuma kafin nan a ka kama Umaru.
Lauyan da ke kare Umaru David Adudu ya roki alfarmar kotun da ta bada belin sa.
Adudu ya kuma tabbatar wa kotu cewa Umaru zai biya kudin belin kuma zai zauna har sai ‘yan sanda sun gama bincike akai.
Alkali Samson Gang ya yanke hukuncin ba Umaru belin naira 200,000 sannan kuma yana bukatan su kawo takardun shaidar biyan haraji, hotunan fasfo guda biyu da kuma Katin zama dan kasa cikin abubuwan da kotun ta bukata.
Alkalin ya daga shari’a zuwa 25 ga watan Mayu.