RIKICIN PDP: PDPn Makarfi ta karyata kafa sabuwar jam’iyya

0

Jam’iyyar PDPn bangaren Makarfi ta karyata rade-radin da ake ta yadawa wai ta na kokarin kafa wata sabuwar jam’iyyar.

Kakakin jam’iyar PDP na bangaren Makarfi Dayo Adeyeye yace ba gaskiya bace wai wasunsu na kokarin kafa wata sabuwar jam’iyya mai suna APDP.

Dayo ya ce su dai ta bangarensu babu irin wannan magana sai dai kila ta bangaren Ali Sheriff.

Ya ce jam’iyyar su na da farin jini a idanuwar jama’a saboda haka bai ga dalilin da zai sa su kafa wata jam’iyya ba.

Share.

game da Author